in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagoran adawa na Sudan ta kudu ya yabawa yunkurin shugabannin nahiyar Afrika na farfado da zaman lafiya a kasar
2018-11-01 11:02:45 cri
Jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu, Riek Machar, ya yabawa kokarin shugabannin Afrika daban-daban, bisa kokarinsu na farfado da tsarin wanzar da zaman lafiya a kasar, bayan barkewar sabon rikici a 2016.

Riek Machar, wanda ke jagorantar kungiyar 'yan tawaye ta 'yantar da al'ummar Sudan ta Kudu ko sojoji 'yan adawa, ya jinjinawa shugaban kasar Sudan Omar al- Bashir da Firaministan Habasha Abiy Ahmad da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da shugaban Uganda Yoweri Museveni, bisa taimakon da suka bayar na ganin bangarorin adawa na kasar Sudan ta Kudu, sun cimma matsayar da ta kai ga samar da yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a Habasha.

Ya kuma mika godiyarsa ga kasashe da kungiyoyi, ciki har da Tarayyar Turai da kungiyar raya yankin gabashin Afrika IGAD da kuma kasar Sin.

Shi ma Shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta Kudu (UNMISS) David Shearer, ya yabawa shugabannin yankin, musammam shugabannin Sudan da Uganda, bisa muhimmiyar rawar da suka taka wajen samar da yarjejeniyar da kuma jagorntar aiwatar da ita.

Ya ce har yanzu da sauran aiki, wanda ya kunshi tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar. (Fa'iza)

David Shearer ya kuma bukaci Sudan ta Kudu ta rungumi aminci a matsayin jigon aiwatar da yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China