in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burkina Faso ya gana da babban jami'in kasar Sin
2019-03-08 10:14:02 cri

Shugaba Christian Kaboré na Burkina Faso, ya gana da tawagar kasar Sin karkashin shugabancin mataimakin shugaban sashen cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwamitis ta kasar Sin Guo Yezhou a birnin Ouagadougou, hedkwatar kasar.

A yayin ganawar a jiya, shugaba Kaboré ya ce, kasarsa na tsayawa tsayin daka kan manufar "kasar Sin daya tak a duniya", kuma tana son yin koyi da tunanin kasar Sin na raya kasa, da kuma kara amincewa da juna tsakanin kasashen 2 ta fuskar siyasa, da kara azama kan hadin gwiwarsu, a kokarin kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri.

A nasa bangaren kuma, mista Guo ya ce, kasar Sin na son hada kai da Burkina Faso wajen aiwatar da muhimman ra'ayoyi daya da shugannin kasashen 2 suka cimma, da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da sa kaimi kan ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen 2 yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China