in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 6 sun mutu a harin bom a Burkina Faso
2018-08-12 15:45:00 cri
Kimanin mutane 6 ne aka hallaka a wani harin bom wanda aka kaddamar kan wata motar jami'an tsaro a lardin Gourma dake gabashin kasar Burkina Faso, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar a jiya Asabar.

A cewar sanarwar, motar tana kan hanyarta ne ta zuwa wata mahakar zinari kafin daga bisani suka afka kan boma baman da aka girke a gefen hanya. Sojoji 5 da farar hula guda ne suka mutu a sanadiyyar harin.

Babu wanda yayi ikirarin daukar alhakin kaddamar da harin.

A farkon wannan shekarar, wasu mahara da ba'a san ko su wane ne ba suka kaddamar da hare hare kan helkwatar rundunar sojojin kasar da kuma ofishin jakadancin kasar Faransa dake Ouagadougou babban birnin kasar , inda yayi sanadiyyar mutuwar sojoji 8.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China