Shugaba Kaboré ya ce, kasashen Afirka suna fatan yin koyi da kasar Sin, musamman ma a fannonin da suka jibanci habaka tattalin arzikin kasa da kyautata zaman rayuwar al'umma.
A cewar Kaboré, ziyararsa kasar Sin a wannan karo za ta karfafa hadin-gwiwa tsakanin Burkina Faso da kasar Sin, gami da hadin-gwiwa tsakanin yammacin Afirka da kasar Sin. Ya kuma yaba sosai da shawarar "ziri daya da hanya daya", abun da ya ce za ta iya inganta mu'amalar cinikayya tsakanin kasashe daban-daban da samar da wadata a duniya baki daya. Ya jaddada cewa, ra'ayin raya makomar bil'adama ta bai daya da shugaban kasar Sin ya fitar ita ma na da babbar ma'ana, wadda ya ce za ta iya fadada hadin-gwiwa da bunkasuwa tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin.(Murtala Zhang)