in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yang ya gana da ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso
2018-05-28 14:07:48 cri

A yau ne, shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa Mista Wang Yang ya gana da ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso Alpha Barry a nan birnin Beijing.

A jawabinsa yayin ganawar, Mr Wang ya jaddada niyyar Sin na hada kai da Burkina Faso, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba zuwa wani sabon matsayi.

Wang Yang ya kuma isar da gaisuwar shugaba Xi Jinping ga shugaba Christian Kaboré na kasar Burkina Faso, kana ya bayyana farin ciki ga sake kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. A cewarsa, Burkina Faso ta amince da manufar kasar Sin daya tilo a duniya da yanke shawarar sake kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Sin matakin da ya dace da yanayin da ake ciki yanzu a duniya, da kuma matsaya daya da yawancin kasashen duniya ke da shi, ko shakka babu tarihi zai shaida gaskiyar wannan mataki. Ya ce, kasar Sin tana maraba da shugaban Burkina Faso ya halarci taron koli na birnin Beijing na dandalin hadin kan kasashen Sin da Afrika da zai gudana a watan Satumba a nan birnin Beijing, tare da fatan Burkina Faso za ta ba da gudunmawarta yadda ya kamata.

A nasa bangare, Barry ya isar da gaisuwar da fatan alheri da shugaba Christian Kaboré ya aiko wa shugaba Xi Jinping. Ya ce, sake kulla dangantakar diplomsiyya da kasar Sin ya dace da halin da ake ciki kuma ya samu amincewar jama'ar kasarsa. Burkina Faso na fari ciki sosai da sake kulla tsarin hadin gwiwa tsakaninta da Sin, haka kuma za ta nace ga manufar kasar Sin daya tilo a duniya da zurfafa hadin kai da kasar Sin tare kuma da ba da gudummawa wajen raya dangantakar dake tsakanin kasahen biyu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China