in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 aka hallaka a Burkina Faso a harin ta'addanci
2019-01-12 15:48:55 cri
Kimanin mutane 12 aka kashe kana wasu mutune biyu suka jikkata a sakamakon wani harin ta'addanci da aka kaddamar a ranar Alhamis a lardin Soum, dake arewacin kasar Burkina Faso, ma'aikatar kwantar da kura ta kasar ce ta sanar da hakan da yammacin jiya Juma'a.

Wasu 'yan bindiga da yawansu ya kai 30 ne suka shirya kai harin da tsakiyar rana, inda suka shirya kai harin kan jama'a a wata kasuwar dake ci sau guda a kowane mako a kauyen Gasseliki, a cewar sanarwar.

An rawaito cewa, maharan sun yi fashi a wasu shaguna sannan suka budewa jama'a wuta.

Babu wani mutum ko kungiya da ta yi ikirarin daukar nauyin harin.

A ranar Juma'a majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da tsawaita dokar ta-baci a wasu yankuna da dama na lardunan arewacin kasar har na tsawon watanni 6 sakamakon yadda mahara ke cigaba da kai hare-hare cikin watannin baya bayan nan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China