Sanarwar ta bayyana cewa, da karfe 4 na sanyin safiyar wannan rana ne, dakarun suka kai hari kan babban sansanin dake arewacin kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji a kalla 4 tare da raunatar mutane da dama. Kana dakarun sun kona wasu gine-ginen sansanin.
Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko mutumin da ya sanar da daukar alhakin kai harin.
Tun daga shekarar 2015, aka kai hare-hare a kasar Burkina Faso, wadanda ke barazana ga halin tsaro a kasar. Ko a ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2018, wasu dakaru sun kai hare-hare ga hedkwatar sojojin kasar dake birnin Ouagadougo da ofishin jakadancin kasar Faransa dake kasar, wadanda suka haddasa mutuwar sojoji 8. (Zainab)