Jiya Talata ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC a nan Beijing, inda firaministan kasar Li Keqiang ya karanta rahoton ayyukan gwamnatin.
Deogratius Kamagi, wakilin jaridar Daily News ta kasar Tanzaniya ya tattara labari kan bikin bude taron, ya kuma mai da hankali kan raya "ziri daya da hanya daya" da aka ambata cikin rahoton. Ya ce ya yi imanin cewa, haduwar "ziri daya da hanya daya" ta kasance kamar wata kyakkyawar dama ga kasarsa. A matsayinta na wadda ta shiga aikin raya "ziri daya da hanya daya", Tanzaniya za ta farfado da kanta, da kara samar da guraben aikin yi, da kyautata zaman rayuwar jama'a ta wannan hanya wadda ke samar da moriyar juna. (Tasallah Yuan)