Mohsen Shariatinia, wani masani harkokin kasar Sin a jami'ar Shahid Beheshiti ta kasar Iran ya bayyana jiya cewa, abin da ya fi burge shi a rahoton ayyukan gwamnatin Sin, shi ne yadda kasar take tinkarar matsaloli da batutuwan masu alaka da tattalin arziki da zaman al'ummar kasar ba tare da rufa-rufa ba, inda kuma ta yi alkawarin ci gaba da warware su ta hanyar raya tattalin arzikin kasar.
Rahoton ya ce, karuwar GDP ta kasar Sin ta kai kaso 6.6 bisa dari a shekarar 2018, yayin da ta tsara wani shiri game da karuwar GDP a shekarar 2019 wato zai kai kaso 6 bisa dari zuwa kaso 6.5 bisa dari.
Yayin da Mohsen Shariatinia yake zantawa da 'yan jarida game da batun na tattalin arziki, ya ce, a shekarun baya, karuwar tattalin arzikin kasar Sin ta ragu sannu da hankali, saboda Sin ta shiga sabon tsarin yau da kullum kan tattalin arziki. Hakan ya nuna cewa, kasar Sin tana neman kara darajar kayayyaki ta hanyar nazarin kimiyya, a maimakon gurbata muhalli, da bata makamashi da yawa, da dogaro da sayar da kayayyaki zuwa ketare. (Tasallah Yuan)