Yau Talata Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya ce, kasarsa za ta kara karfin kyautata muhallin raya tattalin arziki mai zaman kansa, tare da yin adalci a tsakanin dukkan masana'antu a fannonin ba da iznin shiga kasuwar kasar, da sayar da kayaki ga hukumomin gwamnati, da ba da kwangila da neman kwangila da dai sauransu. Ya ce wajibi ne kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan kiyaye 'yancin mallakar fasaha, da hukunta dukkan aikace-aikacen satar fasaha bisa doka, a kokarin ganin 'yan kasuwa sun tafiyar da kamfanoninsu cikin kwanciyar hankali. (Tasallah Yuan)