A cikin rahoton aikin da gwamnatin kasar Sin ta gabatarwa majalisar NPC wadda ta kasance hukumar koli ta kafa doka ta kasar, an nuna cewa, a bana gwamnatin za ta dauki matakai daban daban domin sa kaimi ga karuwar kudin shiga da mazauna birane da karkara za su samu, da ma kara yawan kudin da za a kashe. Sa'an nan za ta kara samar da kayayyaki masu inganci da hidimomi masu kyau ta hanyoyi daban daban domin biyan sabbin bukatun masu sayayya, baya ga gaggauta shigar da kudade masu zaman kai kasuwar kasar.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, yawan tsoffin da shekarusu suka wuce 60 ya kai miliyan 250, don haka gwamnatin za ta kara dora muhimmanci kan aikin kulawa da tsoffi musamman ma irin aiki a unguwanni. A sa'i daya kuma, gwamnatin za ta ci gaba da raya sha'anin yawon shakatawa, da aiwatar da manufar samar da rangwame ga masu sayen motoci masu amfani da sabbin makamashi mai tsabta.(Kande Gao)