in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#2019Taruka2# Kasar Sin za ta kara tuntuba da hadin gwiwa tare da manyan kasashe
2019-03-05 11:22:33 cri

Firaminitan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau Talata cewa, a shekarar 2019, kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da ma manufar bude kofa ga waje don moriyar juna da samun nasara tare, baya ga daukar ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da kiyaye tsarin kasa da kasa dake dora muhimmnaci ga kundin tsarin dokokin MDD. Ban da wannan kuma, Sin za ta ba da gudummawarta wajen aikin kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya, da kiyaye ci gaban tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa ga juna, da raya makomar bil Adama ta bai daya. Haka zakila, Sin za ta kara tuntuba da hadin kai tare da manyan kasashen duniya, da inganta dangantakar dake tsakaninta da makwabtanta, da ingiza hadin kai tare da kasashe masu tasowa don moriyar juna. Bugu da kari ma, Sin za ta kara ba da dabarunta wajen daidaita matsalolin da ke gaban duniya baki daya da ma batutuwan shiyya-shiyya masu jawo hankalin mutane.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China