Rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da aka gabatarwa taron majalisar wakilan jama'ar kasar yau ya jaddada cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin "kasa daya tsarin mulki iri biyu" wato "mazauna Hong Kong su gudanar da harkokin yankinsu da kansu", su ma "mazauna Macao su gudanar da harkokin yankinsu da kansu" bisa doka daga duk fannoni a bana, haka kuma za ta ci gaba da goyon bayan yankunan na musamman biyu wato Hong Kong da Macao domin su shiga shawarar ziri daya da hanya ziri, yadda za ta kara zurfafa hada kan dake tsakanin babban yankin kasar da yankunan biyu.
A sa'i daya kuma, rahoton ya sake nanata manufar da gwamnatin tsakiyar take aiwatarwa kan lardin Taiwan, inda aka jaddada cewa, ya kamata gabobi biyu na zirin Taiwan su kara hada kansu domin samun ci gaba tare, haka kuma su ci gaba da habaka cudanyar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da al'adu.(Jamila)