Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya furta a yau Talata cewar, a bana, kasar Sin za ta kara janyon jarin kasashen waje, da kara sassaucin shigar da 'yan kasuwa baki zuwa cikin kasuwarta, da rage yawan sana'o'i da ayyukan da za a haramta zuba jari a kansu a kasar Sin, da aiwatar da matakan yin gyare-gyare da bude kofa a sha'anin kudi, da kyautata manufar bude kofar kasuwar takardu masu daraja ga ketare, da ma gaggauta aikin bin ka'idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, a kokarin raya muhallin kasuwanci mai adalci, da ma kara kiyaye muradun 'yan kasuwa baki bisa doka.
Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta kara gina wata sabuwar haraba a yankin gwaji na ciniki maras shinge na Shanghai, sa'an nan za ta sa kaimi ga aikin gina yankin gwajin a lardin Hainan, a kokarin raya wata tashar musamman ta sufurin jiragen ruwa mai 'yanci a kasar Sin.(Kande Gao)