in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNEP: Kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen kiyaye muhalli
2019-03-06 10:09:49 cri

Madam Joyce Msuya, mukaddashiyar darektar zartaswa ta hukumar kula da harkokin kare muhalli ta MDD wato UNEP ta ce, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen kare muhalli.

Madam Msuya ta fadi haka ne yayin da take zantawa da wakiliyarmu jiya a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, inda ta kara da cewa, yanzu kasar Sin tana tsara shirin hukumar na kiyaye muhalli a nan gaba, a yayin da ake gudanar da taro na 2 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a Beijing. Ta yi farin ciki da ganin gwamnatin Sin ta kara azama kan daidaita matsalar gurbata muhalli da raya makamashin da ake iya sake amfani da shi.

Za a gudanar da babban taron muhalli na duniya karo na 4 a tsakiyar wannan wata da muke ciki a Nairobi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China