Yau Talata Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya ce, kasarsa za ta kara azama kan kyautata tsoffin masana'antu, da gaggauta raya sabbin masana'antu, da goyon bayan kamfanoni da su kara saurin yin gyare-gyare kan fasaharsu da kuma sabunta injuna, da kara azama kan kaiwa matsayin duniya, da taimaka wa bunkasuwar sabuwar fasahar sadarwa da kuma sabbin masana'antu, da kara karfin tattalin arziki na zamani.
A cikin rahoton ayyukan gwamnati da firaministan kasar Sin ya karanta yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC a yau, ya ce, kasar ta Sin za ta kara hada kai da kasa da kasa ta fuskar kirkire-kirkire, tare da kyautata hidimomin da ake bai wa daliban kasar da suka dawo gida da kuma kwararru 'yan kasashen waje. (Tasallah Yuan)