in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#2019Taruka2# Kasar Sin ta kammala muhimman ayyukan raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta da aka tsara a shekarar 2018
2019-03-05 09:34:07 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana yau Talata cewa, shekarar 2018 shekara ce ta farko da gwamnatin kasar Sin ta wannan zama ta kaddamar da aikinta, duk da kasancewar yanayi mai tsanani da ba a taba fuskantar irinsa ba a shekaru da dama da suka wuce, amma kasar Sin ta kammala muhimman ayyukan raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma da ta tsara yadda ya kamata, kana ta samu sabon ci gaba yayin da take kokarin cimma burin kyautata zamantakewar al'umma mai matsakaiciyar wadata.

A shekarar 2018, karuwar jimillar GDP da kasar Sin ta samu ya kai kashi 6.6%, jimillar kuwa ta zarce Yuan triliyan 90, baya ga yawan matalauta wanda ya ragu zuwa miliyan 13.86.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China