in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#2019taruka2#An yi hasashen karuwar tattalin arzikin Sin a 2019 zai kai 6%-6.5%
2019-03-05 09:54:14 cri

Gwamnatin kasar Sin ta tsara wani shiri game da karuwar GDP a shekarar 2019 wato karuwar GDP a bana zai kai kaso 6 bisa dari zuwa kaso 6.5 bisa dari.

A cikin rahoton aikin gwamnatin da aka gabatarwa taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin domin tantancewa, an yi nuni da cewa, duk da cewa, ana fuskantar yanayi mai tsanani a shekarar da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasar Sin zai kara samun ci gaba mai dorewa, haka kuma gwamnatin kasar za ta ci gaba da kokarin kara samar da guraben ayyukan yi ga al'ummar kasar dake garuruwa da birane, da za su kai miliyan 11, wannan shi ma karo na farko da aka tsara shirin samar da guraben ayyukan yi a cikin rahoton aikin gwamnatin kasar ta Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China