Yau Talata Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya ce, kasarsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin kudi da na hada-hadar kudi yadda ya kamata, a kokarin tabbatar da raya tattalin arzikin kasar da kyau. Gibin kudi da ta lisafta a bana ya kai kashi 2.8 cikin dari, wanda ya karu da kashi 0.2 cikin dari bisa na shekarar 2018, sa'an nan jimillar gibin kudade a baitumalin gwamnatin tsakiya da na kananan hukumomi zai kai kudin Sin RMB yuan triliyan 2.76.
A cikin rahoton ayyukan gwamnati da firaministan kasar Sin ya karanta a yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC a yau, ya ce, kasar Sin za ta kyautata tsarin farashin musayar kudi, a kokarin tabbatar da farashin musayar kudin RMB yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)