Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana yau Talata cewa, gwamnatin Sin za ta ci gaba da rage yawan harajin da za a karba, musamman ma rage yawan harajin da ake karba daga wajen masana'antun kere-kere da kananan kamfanoni. Kana za ta ci gaba da yin kwaskwarima ga tsarin harajin da aka bugawa kayayyakin da aka kara darajarsu, wato za a rage yawan harajin daga kashi 16% a yanzu ya zuwa kashi 13%, domin tabbatar da ganin an rage yawan harajin da aka bugawa muhimman sana'o'i. Game da dukkan sana'o'i, bubu karuwar yawan harajin ko kadan sai dai raguwa, musamman ma yin rangwame ga kananan kamfanoni.(Kande Gao)