Gobe Talata 5 ga watan Maris, za a bude taro karo na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC a takaice ta 13 a babban dakin taron jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing, inda firayin ministan majalisar gudanarwar kasar Li Keqiang zai gabatar da rahoton aikin gwamnatinsa, tare kuma da tantance rahoton gudanar da shirin raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2018, da rahoton daftarin shirin raya tattalin arzikin kasar na shekarar 2019, da rahoton shirin kasafin kudin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kaminis ta kasar Sin da lardunan kasar na shekarar 2018, da kuma rahoton daftarin shirin kasafin kudin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da lardunan kasar na shekarar 2019, kana tawagogin wakilai daban daban za su kira cikakken taro gobe da yamma domin tantance rahoton aikin gwamnatin.
Gobe da safe mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wadanda suka halarci taro karo na 2 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta 13 su ma za su halarci taron, da yamma kuma, za a kira taron kungiya kungiya na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa domin tattauna rahoton aikin gwamnatin.
Babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG zai nuna bikin bude taro karo na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 kai tsaye, kana shafukan yanar gizo da dandalin sada zumunta na muhimman kafofin watsa labarai na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin su ma za su watsa labaran da abin ya shafa kai tsaye daya bayan daya.(Jamila)