in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin da kasar Sin ta kashe ta fuskar aikin soja ba zai kawo barazana ba
2019-03-04 16:06:47 cri

Kakakin taro na 2 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 13 Zhang Yesui, ya ce kudi kalilan da kasar Sin ta kashe ta fuskar aikin soja ba zai kawo wa sauran kasashe barazana ba.

Zhang Yesui ya shaidawa wani taron manema labarai a yau cewa, kudin da kasar Sin ta kashe ta fuskar aikin soja a shekarar 2018 ya kai kashi 1.3 cikin dari bisa jimilar kudaden da aka samu daga wajen sarrafa dukiyoyin kasar Sin wato GDP, yayin da irin wannan kudi ya wuce kashi 2 cikin dari bisa jimilar GDP na wasu kasashe masu ci gaba. Ya ce har kullum, kasar Sin na kan hanyar raya kasa cikin lumana, kuma manufar tsaron kasar ita ce kare kanta. Ta kashe kudi kalilan wajen aikin soja ne domin kiyaye ikon mulkin kasa, tsaron kasa, da cikakkun yankunan kasa, wanda ba zai kawo wa sauran kasashe barazana ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China