Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi kira ga marubuta da masu fasaha da masu tsara manufofi da su karfafa harkokin al'adu, da samarwa jama'a ayyuka masu kyau da yiwa al'umma jagora da kyawawan dabi'u.
Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin koli na rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne lokacin da ya halarci taron tattaunawar da ya samu halartar masu ba da shawara kan harkokin siyasa daga sassan al'adu da fasaha da kimiyyar zamantakewar al'umma. Mashawartan dai suna halartar taro na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 13 dake gudana a halin yanzu.(Ibrahim)