Wu Weiren ya bayyana cewa, dukkan abubuwan da aka gano a duniyar wata sabon ilmi ne da dan Adam ke samu, wanda yake da babbar daraja a fannin kimiyya da fasaha.
Ya bayyana wa 'yan jarida cewa, ana sa ran za a dawo da kasar da aka samu a duniyar wata a karshen shekarar 2019, ta hakan Sin za ta kasance kasa ta uku a duniya da ta dawo da kasar duniyar wata zuwa duniyar kasa bayan Amurka da tarayyar Soviet. A shekarar 2020, kasar Sin za ta harba na'urar bincike da za ta sauka a duniya Mars tare da gudanar da bincike a can.
Ya kara da cewa, sha'anin binciken sararin samaniya sha'ani ne na dan Adam, za a bayyana abubuwan da aka binciko ga dukkan duniya, don samar da gudummawa wajen yin amfani da sararin samaniya cikin lumana da sa kaimi ga raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, kana ana fatan kasa da kasa za su hada kai da shiga shirin binciken sararin samaniya. (Zainab)