in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin zata tabbatar da yin amfani da kowane kwabo yadda ya kamata yayin da take taimakawa kasashen waje
2019-03-03 20:30:23 cri

Shugaban hukumar hadin gwiwa da kasashen waje don neman ci gaba baki daya ta kasar Sin Mr. Wang Xiaotao ya bayyana yau Lahadi a birnin Beijing cewar, tun bayan da aka kafa hukumar a bara, koda yaushe tana aiwatar da manufar "cimma muradu da kuma martaba ka'idoji" wajen cudanyar kasashen waje domin ci gaba da samar da taimako ga dimbin kasashe masu tasowa gwargwadon karfinta. Lamarin da yasa kasar Sin ta samu yabo daga gamayyar kasashen duniya.

Bugu da kari Wang ta furta cewa, kawo yanzu dai kasar Sin kasa ce mai tasowa, akwai rashin daidaito a tsakanin yankuna daban daban da birane da karkara wajen bunkasuwa, wadda take daukar babban nauyin samun bunkasa da kyautata rayuwar jama'a. Saboda haka, kasar Sin zata taimakawa sauran kasashe bisa karfin kanta, da kuma tabbatar da yin amfani da kowane kwabo yadda ya kamata.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China