in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala share fagen taro na 2 na NPC karo na 13
2019-03-04 14:06:19 cri

Yau Litinin da safe ne aka gudanar da taron share fagen taro na 2 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo na 13, inda Li Zhanshu, shugaban zaunannen kwamitin NPC ya shugabanci taron, wanda ya sanar da cewa, za a bude taro na 2 na majalisar NPC karo na 13 gobe Talata 5 ga wata. Yanzu a shirye ake wajen bude taron.

Bisa ajandar da aka tsai da, an ce, za a duba tare da tattauna rahoton ayyukan gwamnatin a yayin taron da za a bude gobe, haka kuma za a duba yadda aka tafiyar da shirin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa na shekarar 2018 da kuma daftarin shirin na shekarar 2019. Sa'an nan kuma, za a duba yadda aka aiwatar da kasafin kudi na gwamnatin tsakiya da kananan hukumomi a shekarar 2018, da kuma daftarin kasafin kudi na shekarar 2019. Za a kuma duba tare da tattauna daftarin shiri kan zuba jari da 'yan kasuwan waje suka yi, da rahotannin ayyukan zaunannen kwamitin NPC, da na babban kotun jama'ar kasar, da na babbar hukumar kai kara ta jama'ar kasar da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China