in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kula da shawarwari kashi 99.2 cikin dari da aka gabatar gaban majalisar CPPCC
2019-03-04 11:21:01 cri
Bayan gudanar da taro na farko na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 13, yawan shawarwarin da membobin majalisar da hukumomi masu halartar majalisar da kwamitocin musamman suka gabatar a gaban majalisar ya kai 5360, yawansu da aka gabatar ba a gun taron majalisar ba ya kai 211. Bayan gudanar da bincike, yawan shawarwarin da aka tsaida kudurin aiwatar da su ya kai 4567, wadanda aka mika ga hukumomi 165 don aiwatarwa. Ya zuwa ranar 20 ga watan Febrairuna bana, an samu sakamako wajen kula da kashi 99.2 cikin dari na shawarwarin da aka gabatar.

Mataimakiyar shugaban majalisar CPPCC Su Hui ta yi bayani game da yanayin kula da shawarwarin da aka gabatar a taro na farko na majalisar CPPCC karo na 13 a gun taro na biyu na majalisar bisa iznin da zaunannen kwamitin majalisar CPPCC karo na 13 ya ba ta. Ta bayyana cewa, sakamakon kokarin da bangarori daban daban suka yi, an kula da shawarwarin da aka gabatar tare da samun sakamako, wadanda suka samar da gudummawa wajen tsaida kuduri da sa kaimi ga aiwatar da ayyuka yadda ya kamata.

Su Hui ta kara da cewa, a shekarar 2019, za a ci gaba da kula da shawarwarin da aka gabatar yadda ya kamata, da maida hankali ga aiwatar da su da kyau, da kara kyautata tsari da daukar matakai don kara taka muhimmiyar rawa ga aikin majalisar CPPCC a fannin gabatar da shawarwari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China