Kakakin taro na 2 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 13, Zhang Yesui, ya ce hadin gwiwa ita ce zabi mafi dacewa ga Amurka da Sin, yayin da yin fito na fito ba zai amfanawa bangarorin biyu ba.
Zhang Yesui ya shaidawa wani taron manema labarai a yau cewa, samun sabani tsakanin Amurka da Sin ba wani abu ba ne, amma ba sai ya kai matsayin fito na fito ba, yana mai cewa moriyar kasashen biyu na hade ne da juna.
Ya ce kasar Sin ta kuduri niyyar kulla dangantaka da Amurka, ta mutuntawa da moriyar juna, wadda za ta kaucewa rikice-rikice da sabani, a daya bangaren kuma, kasar za ta tsaya kan bakanta na kare 'yanci da tsaro da muradunta na ci gaba.
Ya kara da cewa, wakilan kasashen biyu dake tattauna harkokin cinikayya da tattalin arziki sun yi tattaunawa mai zurfi da fa'ida , kuma sun samu ci gaba game da batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya.
Ya ce sun yi amana dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka na da nufin cimma moriyar juna, a don haka suke fatan bangarorin biyu za su ci gaba da matse kaimi wajen tuntubar juna domin cimma yarjejeniyar da baki dayansu za su amfana. (Fa'iza Mustapha)