in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Margaret Chan Fung Fu-chun: iyawar kasar Sin ta shawo kan cuta mai yaduwa tana kan gaba a duniya
2019-03-03 20:40:20 cri

'Yar majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC Madam Margaret Chan Fung Fu-chun ta bayyana yau Lahadi cewa, iyawar kasar Sin ta shawo kan cututtuka masu yaduwa tana gaba a duniya.

Madam Chan ta kara da cewa, yayin da take aiki a hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO a matsayin babbar daraktar hukumar, ta taba yin kira ga kowace kasa da kowane yanki dasu kafa tsarin shawo kan cututtuka masu yaduwa. Lallai kasar Sin ta yi gaba a wannan fanni a duk fadin duniya. Alal misali, kungiyar bada agajin gaggawa ta kasar Sin tana daya daga cikin kungiyoyin agajin da hukumar WHO ta amince dasu. Lamarin da ya shaida cewa, kwarewa da iyawar kasar Sin a fannin shawo kan cututtuka masu yaduwa tana matsayin koli a duk duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China