in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na CPPCC
2019-03-03 16:01:01 cri

An kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin ko kuma CPPCC a takaice yau Lahadi a birnin Beijing, inda shugaban kasar Xi Jinping gami da sauran shugabannin kasa da na jam'iyyar kwaminis ta kasar suka hallara.

Shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, Wang Yang ya gabatar da wani rahoton aiki a madadin zaunannen kwamitin majalisar, inda ya jaddada cewa, bana, muhimmiyar shekara ce ta kyautata zamantakewar al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, inda kamata yayi majalisar CPPCC ta taka muhimmiyar rawarta wajen maida hankali kan wasu muhimman ayyuka, ciki har da kyautata zamantakewar al'umma mai matsakaicin wadata, da shawo kan wasu manyan haddura, da tallafawa matalauta, da kiyaye muhallin halittu. Haka kuma, ya zama dole majalisar CPPCC ta sauke nauyin dake wuyanta a fannonin da suka shafi bada shawarwari kan harkokin siyasa, da sa ido bisa tafarkin demokuradiyya, da shiga cikin harkokin siyasa da sauransu.

Za'a shafe tsawon kwanaki 11 ana yin zama na biyu na taro karo na 13 na majalisar CPPCC a bana, inda membobi sama da 2100 daga jam'iyyun demokuradiyya da kungiyoyi da kabilu daban-daban na kasar Sin zasu duba rahoton aikin da Wang Yang ya gabatar, da saurare gami da tattaunawa kan rahoton aikin gwamnati, tare kuma da bada shawarwari da nasihohi ga manufofin yin gyare-gyare da neman ci gaba na kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China