An yi maraba da ci gaban da aka samu tsakanin Sin da Amurka game da tattaunawar harkokin cinikayya da tattalin arziki
Kakakin cikakken zama karo na 2 na majalisar bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin ta 13 Mr. Guo Weimin, ya yi maraba da nasarar da aka samu dangane da tattaunawar da ake tsakanin Sin da Amurka kan harkokin cinikayya da tattalin arziki.
Guo Weimin, ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, cimma yarjejeniyar moriyar juna ba kasashen biyu kadai zai amfanawa ba, har ma da duniya baki daya.
Kakain ya kara da cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ta samar da ci gaba da kyakkyawan fata ga kasashen da suka shiga shawarar. (Fa'iza Mustapha)