in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude cibiyar watsa labarai don share fagen tarukan majalisun kasar Sin na bana
2018-02-27 13:30:14 cri

Za a kaddamar da taron majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta wannan shekara a ranar 5 ga watan Maris, gami da taron majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar a ranar 3 ga watan mai zuwa. Domin share fagen muhimman tarukan 2, a yau Talata ne aka bude wata cibiyar kafofin watsa labarai a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda za a samar da hidima ga 'yan jaridu na kasar Sin da na kasashen waje, wadanda ke da aniyar rubuta bayanai dangane da tarukan 2 da za su gudana. Haka zalika, a tarukan 2 na wannan shekara, za a kebe wani wuri na musamman domin wakilan jama'ar kasar Sin su bayyana ra'ayoyinsu ga manema labaru.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China