in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nanata bukatar warware rikicin Syria ta hanyar siyasa
2017-05-03 20:14:41 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya furta a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, hanyar siyasa ita ce hanyar daya tilo da za a iya bi don warware rikicin kasar Syria.

Yanzu haka dai ana gudanar da taron yini biyu tsakanin Larabar nan zuwa gobe Alhamis, musamman domin zakulo hanyar warware rikicin Syria, taron dake gudana a birnin Astana, fadar mulkin kasar Khazakstan.

Rahotanni dai na nuna cewa mahalarta taron na da sabanin ra'ayi game da wasu batutuwa masu yawa.

Game da hakan ne kuma, Mr. Gang Shuang ya ce, makasudin taron shi ne kokarin tabbatar da kudurin tsagaita bude wuta a Syria, kuma kasar Sin na fatan ganin bangarorin masu ruwa da tsaki za su yi amfani da wannan dama, domin kara musayar ra'ayi, da nuna sahihanci, gami da tabbatar da amincewa juna, ta yadda za a share fagen shawarwarin da za a gudanar nan gaba, da samar da gudunmowa ga yunkurin daidaita rikicin kasar ta Syria a siyasance. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China