in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin sufurin jiragen saman Habasha ya yi hasashen samun bunkasuwa a kasuwannin kasar Sin
2019-03-01 10:50:15 cri

Kamfanin sufurin jiragen sama na kasar Habasha wato Ethiopian Airlines (ET), ya yi hasashen samun bunkasuwa sama da wanda yake da shi a yanzu a kasuwannin sufurin jiragen sama na kasar Sin, wani jami'in kamfanin ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, Esayas Woldemariam, manajan daraktan harkokin sufuri na kasa da kasa na ET ya ce, da ma tuntuni kamfanin yana zirga-zirga zuwa wurare biyar na kasar Sin, amma ya jima yana burin fadada zirga-zirga zuwa karin wasu sassan kasar Sin.

Woldemariam ya kara da cewa, kamfanin Ethiopian Airlines yana shirin fadada zirga-zirgarsa zuwa biranen Dalian, Zhengzhou da Hangzhou, matakin zai taimaka wa kamafanin na ET hadewa yankunan gabashi, tsakiya da kuma arewacin kasar Sin.

Haka zalika, Woldemariam ya ce, kamafanin na Ethiopian Airlines ba wai yana daukar kasar Sin a matsayin wurin yawon shakatawa ba ne kadai, har ma a halin yanzu, ya fara tattaunawa da wasu takwarorinsu na kasar Sin domin yin hadin gwiwar kasuwanci.

ET ya riga ya tattauna da kamfanonin sufurin jiragen saman kasar Sin domin sanya hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyi.

Karkashin wadannan yarjejeniyoyi, kamfanonin sufurin jiragen saman kasar Sin za su iya daukar fasinjojin kamfanin ET, domin kai su wuraren da za su je a duk fadin kasar Sin. Kamfanonin sufurin jiragen saman biyu daga bisani za su kasafta kudaden da aka samu a hada-hadar.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China