Jiragen kamfanin dai za su fara jigilar fasinjan ne tun daga ranar 22 ga watan Mayun nan, wanda hakan ke nuna karuwar sassa da jiragen kamfanin za su rika zuwa a cikin kasar Sin ya zuwa birane 5.
Chengdu dai birni ne da ya yi suna wajen yawon bude ido, ana kuma yawan ziyartar sa domin kallon dabbobin panda, da kuma wasu muhimman wurare na tarihi da birnin ke da su.
Cikin wata sanarwa da aka fitar, kamfanin na Ethiopian Airlines, ya ce zai kaddamar da fara wannan jigila ta fasinjoji zuwa birnin Chengdu ne a kan idanun jakadan Sin dake Habasha La Yifan, da shugaban kamfanin jiragen saman na Habasha Tewolde Gebremariam, da kuma kakakin majalissar dokokin kasar Abadula Gemeda, yayin wani biki da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa.
Baya ga birnin na Chengdu, kamfanin jiragen saman na Habasha na zuwa biranen Beijing, da Hong Kong, da Shanghai da kuma birnin Guangzhou dake lardin Guangdong, birnin da ya shahara a fannin hada hadar kayayyakin da masana'antun kasar Sin da dama ke kerawa.(Saminu)