in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Habasha tana fatan za a kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin sufurin jiragen sama
2017-07-23 13:38:34 cri
Ministan harkokin sufuri na kasar Habasha Ahmad Shid ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya cewa, kasar Habasha tana kokarin ganin ta zama cibiyar zirga-zirgar jiragen sama a nahiyar Afirka, kuma tana fatan kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin don cimma wannan buri.

A ganin Shid, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Habasha a fannin sufurin jiragen sama zai kasance wani muhimmin fanni na hadin gwiwar kasashen biyu.

A halin yanzu, kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Habasha ya mai da muhimmanci sosai a kan kasar Sin, don haka kamfanin ya bude hanyoyin jiragen sama na zuwa biranen Beijing, Shanghai, Guangzhou, Chengdu da yankin Hongkong na kasar Sin.

Kana Shid ya bayyana cewa, kasar Sin tana kokarin kasancewa muhimmiyar cibiyar kera jiragen sama ta duniya, kana kasar Habasha tana fatan zama babban abokin ciniki na kasar Sin ta wannan fanni.

Ban da wannan kuma, Shid ya yi bayani cewa, don kara inganta sha'anin sufurin jiragen sama, kasar Habasha tana shirin kara gina wani filin jiragen sama na kasa da kasa a karkarar birnin Addis Ababa, kuma ana saran zuba jari na dala biliyan 3 don gina shi, wanda zai karbi mutane miliyan 100 a kowace shekara. Shid yana fatan samun hadin gwiwar kasar Sin a wannan aiki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China