in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta kaddamar da yankin masana'atu da kasar Sin ta gina a yammacin kasar
2018-12-09 16:30:58 cri

Kasar Habasha ta kaddamar da yankin masana'antu na Jimma, da kasar Sin ta gina a garin Jimma dake yammacin kasar, wanda ke da tazarar kilomita 350 daga Addis Ababa babban birnin kasar.

Ana sa ran yankin masana'antun na Jimma da ya mamaye fili mai kadada 75, zai samu masu zuba jari a fannin masana'antu da suka fi mayar da hankali kan sarrafa amfanin gona da bangaren masaku da tufafi.

Da yake kaddamar da yankin a jiya, Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya ce yankin zai taimakawa yammacin kasar wajen zama daya daga cikin yankunan masana'atu da kasar ke da su.

A cewarsa, yankin wanda shi ne na baya-bayan nan cikin burin kasar na samar da yankunan masana'antu, zai taimakawa jama'ar yankin, musammam matasa ta hanyar samar musu da dubban damarmakin aikin yi.

Da yake bayyana cewa yanzu masu zuba jari na kasashen waje na tuntubar gwamnatin kasar da nufin zuba jari a yankin masana'antu na Jimma, Firaministan ya bukaci al'ummar garin su dage tare da kokarin gwamnatin kasar, wajen karewa da amfana daga yankin masa'antun da kuma kamfanonin da za a kafa a ciki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China