Kasar Habasha ta sanar da kaddamar da rukunin masana'antu na Hawassa da kasar Sin ta gina, wanda aka tsara tare da gina shi ta yadda zai dace da kare muhalli, inda kuma zai zama abun koyi ga sauran rukunin masana'antu da ake ginawa a fadin kasar.
Ana sa ran rukunin masana'antun na Hawassa zai fara aiki cikin mako mai zuwa, kuma zai zama irinsa na farko dake samar da yaduka da kayakin sawa mai ingantacciyar fasaha da kayakin aiki na zamani.
Kasar na fatan da zarar rukunin Hawassa ya fara aiki zai taimakawa kudurin samar da wani bangare na tattalin arziki da zai rage gurbatar muhalli.
An tsara tare da gina shi ta yadda zai dace da kare muhalli sannan ya na da wata fasahar zamani dake sake sabunta kashi 90 na ruwan da zai yi amfani da shi. (Fa'iza Mustapha)