in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta dauki kasar Sin a matsayin babbar kasuwar fitar da hajojinta a bangaren masana'antu
2018-10-26 10:52:24 cri

Wani jami'in kasar Habasha ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasarsa tana daukar kasar Sin a matsayin waje mafi girma na fitar da kayayyakinta domin bunkasa cigaban fannin masana'antun kasar.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Wondimu Filate, shugaban sashen hulda da jama'a da harkokin yada labarai na ofishin ministan cinikin kasar Habasha (MoT), ya ce mafi yawan kayayyakin da kasar Habasha ke fitarwa zuwa ketare kayayyakin amfanin gona ne, da kayayyakin da masana'antu ke bukatarsu, amma galibin kayayyakin da ba'a sarrafa su ba, da kuma wadanda aka kammala sarrafawa ana fitar da su ne zuwa babbar cibiyar kasuwanci mafi girma ta nahiyar Asiya.

Habasha tana fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin wadanda darajarsu ta kai dala miliyan 248 a shekarar 2017/18, ya zuwa 7 ga watan Yulin bana.

Kayayyakin da kasar Habasha ta fitar zuwa kasar Sin a shekarar da ta gabata ya kunshi kayan amfanin gona, da na masana'antu da sauran albarkatu kamar su kofi, da amfanin gonar da ake fitar da mai, da ridi, da fatu, da sinadarin tantalum.

"Kasar Sin ta riga ta zama babbar hanyarmu ta samun jarin kai tsaye na kasashen waje na (FDI), kuma babbar abokiyar cinikayyarmu. Kwararrun masanan kasar Sin da kudaden kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan kafa rukunin masana'antu a duk fadin kasar Habasha, don haka za mu iya cewa Habasha da Sin suna da mu'amalar tattalin arziki mai karfi," in ji Filate.

Kasar Habasha tana samun karuwar cin gajiyar kudade da fasahohin kasar Sin a yayin da take kara adadin rukunin masana'antun kasar daga guda biyar da ake da su a halin yanzu zuwa kusan guda 30 nan da shekarar 2025.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China