in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Habasha ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin
2019-01-04 11:01:21 cri
Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed, ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, a Addis Abeba, fadar mulkin kasar Habasha, a jiya Alhamis.

Yayin ganawarsu, mista Abiy Ahmed ya ce, yadda ministan harkokin wajen kasar Sin ya ziyarci Habasha a farkon wata shekara, ya shaida cewa, kasar Sin sahihiyar aminiya ce ta kasar Habasha, gami da jama'ar kasashen Afirka duka. Sa'an nan kasar Sin tana samar da gudunmowa ga kokarin kasar Habasha, da na sauran kasashen dake nahiyar Afirka na raya kansu. Jami'in ya nanata cewa, kasar Habasha tana tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, haka kuma tana goyon bayan shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Sa'an nan, mista Abiy shi da kansa yana cikin shiri, domin halartar wani taron manyan jami'ai dangane da hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" wanda zai gudana karo na biyu a kasar Sin.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce, Kasar Habasha muhimmiyar abokiya ce ta kasar Sin, musamman ma a fannin aiwatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" a nahiyar Afirka. Ya ce yana da imani kan cewar hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Habasha zai tabbatar da wata kyakkyawar makoma ga huldar dake tsakanin kasashen 2, kuma za ta kara azama ga hadin kan Sin da Afirka karkashin tsarin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Jami'in na kasar Sin ya ce, yana fatan ganin bangarorin 2 su kara kokarin aiwatar da sakamakon da aka samu, yayin taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a kasar Sin bara, gami da shirye-shiryen hadin kai tsakaninsu, don kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, wadda za ta dace da wani sabon yanayin da duniyarmu ke ciki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China