in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin ministocin harkokin wajen Sin da Rasha
2019-02-27 11:26:36 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin kuma mamban majalisar gudanarwar kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov, a garin Wuzhen da ke lardin Zhejiang a jiya Talata. Sergei Lavrov ya zo kasar Sin ne don halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Rasha da Indiya.

A yayin ganawarsu, Wang Yi ya ce, a bana ake cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar Sin da kuma kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Rasha. Don haka, wajibi ne kasashen 2 su share fage sosai kan ganawar da shugabannin kasashen 2 za su yi a bana, tare da shirya wasu abubuwa na murnar cika shekaru 70 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen 2. Wang Yi, ya ce kasashen Sin da Rasha sun kulla huldar abota da hadin gwiwa a tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare, kuma kamata ya yi su kara inganta tuntubar juna a kokarin ba da sabuwar gudummawa wajen kara azama kan samun zaman lafiya da ci gaba a duniya. Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana son hada hannu da Rasha da Indiya wajen samun kyakkyawan sakamakon yayin ganawar.

A nasa bangaren, Lavrov ya yaba da ra'ayin Wang Yi kan huldar da ke tsakanin kasashen 2 da kuma shawararsa. Inda ya ce, wajibi ne Rasha da Sin su kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori daban daban da kuma manyan ka'idojin huldar kasa da kasa. Ya ce Rasha za ta hada kai da Sin da Indiya wajen raya hadin gwiwarsu zuwa sabon mataki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China