in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai dimbin damarmakin fadada dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha
2018-11-16 11:18:19 cri

Firaministan Sin Li Keqiang, ya ce dangantaka tsakanin kasar sin da Rasha a fannoni daban-daban, ta haifar da sabbin sakamako, kuma har yanzu akwai damarmakin fadada ta.

Yayin ganawarsa da Shugaban Rasha Vladimir Putin a jiya Alhamis, a wani bangare na jerin taruka kan kawancen kasashen gabashin Asiya, Li Keqiang ya gabatar da gaisuwar Shugaba Xi Jinping zuwa ga Shugaba Putin, yana mai tunawa cewa shugabanni biyu sun gana sau da dama a bana, kuma sun cimma sabbin yarjeniyoyi.

Da yake bayyana dangantakar kasashen biyu a matsayin mai muhimmanci, Li Keqiang, ya ce taro na 23 tsakanin shugabannin gwamnatocin Sin da Rasha da aka yi a makon da ya gabata a nan birnin Beijing, ya ingiza hadin gwiwa a bangarori da dama da za su kai ga sabbin nasarori.

Har ila yau, ya ce kasar Sin na fadada hadin gwiwarta da Rasha a fannonin cinikayya da zuba jari da makamashi da kirkire-kirkire da harkokin kudi da sauran wasu fannoni.

A nasa bangaren, Shugaba Putin, ya ce a shirye Rasha take ta aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da suka cimma da kasar Sin, tare da kokarin samun sakamako daga hadin gwiwa a fannonin makamashi da sufurin jiragen sama da sararin samaniya da kimiyya da fasaha da tsarin tattalin arziki na zamani. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China