in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Rasha sun amince da zurfafa ayyuka na karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu
2018-09-12 10:03:21 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaran sa na Rasha Vladimir Putin, sun lashi takobin daukar karin matakai, na karfafa hadin gwiwar kasashen su, ta yadda hakan zai amfani al'ummun su yadda ya kamata.

Shugabannin biyu sun tabbatar da hakan ne a jiya Talata, yayin wani zama na shawarwari, a gefen taron dandalin tattauna harkokin tattalin arziki na gabashin kasashen duniya karo na 4, dake gudana a birnin Vladivostok na kasar Rasha.

Da yake tsokaci kan hakan, shugaba Xi ya ce Sin da Rasha, kasashe ne manya dake makwaftaka da juna, sun kuma kasance muhimman abokan hulda na kut da kut, wadanda ke da buri iri daya. Ya ce zai yi ma'anar gaske idan suka mai da hankali ga daukar matakan dakile kalubale da ka iya bullo musu daga waje, su kuma habaka sassan ci gaba da suka shafi kasashen, kana su bunkasa hadin gwiwa, da zurfafa matakan hade muradun su waje guda.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, kudurorin ci gaba na kasashen biyu, suna da matukar muhimmanci ga kyakkyawan hadin gwiwa bisa matsayin koli tsakanin sassan biyu.

A nasa bangare, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ce yana farin ciki game da yadda yankunan dake kewaye da kasashen biyu, ke raya harkokin tattalin arziki da cinikayya cikin hadin gwiwa, baya ga musaya tsakanin al'ummun su da kuma raya al'adu.

Ya ce Rasha na maraba da 'yan kasuwar Sin a fannin zuba jari, kuma kasar sa za ta ci gaba da samar da kyakkyawan muhallin gudanar da mu'amala yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen na Sin da Rasha. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China