in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron manema labarai game da taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin gabashin duniya da shugaba Xi Jinping zai halarta
2018-09-07 13:20:40 cri
Yau Jumma'a, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labarai, game da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Rasha, domin halartar taron dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin gabashin duniya karo na 4.

A yayin taron, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Hanhui ya bayyana cewa, shugaban Sin Xi Jinping, zai halarci taron da za a yi a birnin Vladivostok na kasar Rasha tsakanin ranar 11 zuwa ranar 12 ga watan Satumba da muke ciki.

Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya halarci wannan taro, kuma zai zama muhimmiyar mu'amalar dake tsakanin shugabannin kasashen Sin da Rasha cikin karshen rabin shekarar bana.

Bugu da kari, Zhang Hanhui ya ce, halartar shugaba Xi taron tattaunawar tattalin arzikin gabashin duniya karo na 4, ya nuna kyakyyawan zumuncin gargajiya dake tsakanin kasar Sin da kasar Rasha, wajen nuna goyon baya ga juna cikin manyan harkokin kasa da kasa, lamarin da zai ci gaba da karfafa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yayin da hakan zai inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni. Haka kuma, taron zai samar da damammaki ga kasashen biyu, wajen cimma sabbin sakamako bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasashe mafiya yawa dake gabashin Asiya, da kuma karfafa hadin gwiwar kasashen yankin kan harkokin kiyaye zaman lafiya, da neman ci gaba, da kyautata zaman rayuwar al'umma. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China