in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Rasha za su kara zurfafa mu'amala
2018-08-03 10:14:37 cri
Jami'in majalisar kolin kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya sanar da cewa, Sin da Rasha za su cigaba da daukar kwararan matakan da suka dace domin ciyar da matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba zuwa matsayin muhimmiyar hadin gwiwa daga dukkan fannoni.

Ministan yayi wannan tsokaci ne a lokacin ganawa da takwaransa ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, a gefen taron ministocin harkokin wajen kungiyar ASEAN dake taro da kuma tattauna sauran batutuwa.

Wang ya bayyana cewa, shugabannin Sin da Rasha sun cimma wata muhimmiyar sabuwar matsaya a lokacin ganawarsu a taron BRICS a kasar Afrika ta kudu, ya kara da cewa, wannan ya nuna a fili yadda kasashen Sin da Rasha suka kasance muhimman abokan huldar juna. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China