in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Rasha
2018-09-11 20:32:56 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a garin Vladivostok da ke Rasha, inda shugabannin kasashen biyu suka amince da cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta kara samun bunkasuwa a bana.

Duk da canje-canjen da duniya ke fuskanta, Sin da Rasha za su ci gaba da raya dangantakarsu da ma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

A yayin shawarwarin, Shugaba Xi ya nuna cewa, bangarorin biyu suna nuna goyon baya ga juna wajen bin hanyar raya kasa da ta dace, da kiyaye tsaronsu da 'yancinsu na ci gaba, wanda ya zama abin koyi ga duniya kan yadda ya kamata a raya dangantaka a tsakanin manyan kasashe, da kasashe makwabta. Xi ya kuma jaddada cewa, Sin da Rasha za su kyautata hadin kansu a fannonin makamashi, ayyukan gona, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da ma sha'anin kudi bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da kuma laimar kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya.

A nasa bangaren, Shugaba Putin ya bayyana cewa, bangarorin biyu za su ci gaba da hada kai a fannonin zuba jari, makamashi, zirga-zirgar sararin samaniya, sha'anin kudi, da cinikin Intanat a karkashin inuwar kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya da ma shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kara cudanyar mutane, da ma kara azama wajen hadin gwiwar kananan wuraren kasashen biyu. Ya kuma furta cewa, Rasha da Sin na da ra'ayi daya kan halin da kasashen duniya ke ciki yanzu, ya kamata su kara hadin kai a cikin lamuran duniya, da yaki da ra'ayin kashin kai, a kokarin kiyaye dokokin kasa da kasa cikin adalci da samun wadata gaba daya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China