Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, sun shafe sa'o'i da dama tare a birnin Tianjin na kasar Sin, inda suka halarci bikin maraba tare da yin shawarwari. Baya ga haka, shuagaba Xi Jinping ya karrama tare da ba da lambar abota ta Jamhuriyar jama'ar kasar Sin ga Vladimir Putin, lamarin da ya nuna kyakkyawar huldar zumunta dake tsakanin kasashen biyu.
A yau 9 ga wata ne kuma, za su sake haduwa a birnin Qingdao na kasar Sin don halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai. (Maryam)