Firaministar Birtaniya Theresa May, ta tabbatar da kara dage kada kuri'a kan yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai zuwa ranar 12 ga watan Maris
Da take ganawa da manema labarai a kan hanyarta ta zuwa Sharm el-Sheikh na Masar, domin halartar taron Tarrayar Turai da na kungiyar kawancen Larabawa, Theresa May ta soke batun gabatar da yarjejeniyar ga 'yan majalisar dokokin kasar a wannan mako.
Firaministar ta bayyana cewa, tawagarta za ta koma Brussels a ranar Talata. A don haka, ba za su samu kuri'ar da suke bukata ba a wannan mako, amma za su tabbatar da hakan a ranar 12 ga watan Maris.
Har ila yau, ta ce har yanzu batun barin EU a ranar 29 ga watan Maris ya na hannunsu, kuma shi ne abun da suke shirin yi. (Fa'iza Mustapha)