'Yan majalisar sun kada kuri'ar amincewa 258, da na kin amincewa 303, wanda kuma ke jaddada cewa 'yan Majalisar na sane da tattaunawar dake tsakanin Birtaniya da Tarayyar Turai game da iyakar arewacin Ireland da Jamhuriyar Ireland.
Masu ra'ayin rikau kuwa sun kauracewa kada kuri'ar ne bisa dogaro da cewa, kudurin na nufin soke batun cimma yarjejeniya game da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.
Shugaban Jam'iyyar Labor Jeremy Corbyn, ya yi kira ga Firaministar da ta amince dabararta ta ficewar kasar daga EU ta sha kaye.
Ya ce kuri'u sun nuna cewa matakin na Firaministan ba shi da rinjaye. (Fa'iza Mustapha)