A ranar 15 ga wata, majalisar wakilai ta kasar Birtaniya za ta jefa kuri'u game da yarjejeniyar janyewa daga kungiyar EU, wadda gwamnatin kasar Birtaniya da kungiyar EU suka cimma daidaito.
A ranar 14 ga wata, May ta yi kashedi cewa, idan majalisar wakilai ta kasar ta ki amincewa da yarjejeniyar, yadda Birtaniya ta gaza janyewa daga kungiyar EU, hakan zai kawo illa ga imanin al'ummun kasar ga gwamnati.
May ta kara da cewa, wasu membobin majalisar suna son jinkirta, ko dakatar da janyewa daga kungiyar EU. Idan aka dakatar da yarjejeniyar, watakila kasar Birtaniya ba za ta janye daga kungiyar EU ba, yiwuwar batun ya fi yiwuwar janyewa daga kungiyar EU ba tare da cimma yarjejeniyar ba. (Zainab)